logo

HAUSA

An kone muggan kwayoyi a birane 3 na Myanmar

2022-06-27 13:52:09 CMG Hausa

Kasar Myanmar ta kona wasu muggan kwayoyi da aka kwace a biranen Yangon da Mandalay da Taunggyi a jiya Lahadi, albarkacin ranar yaki da sha da fataucin muggan kwayoyi ta duniya.

Kwayoyin da aka lalata sun hada da na tabar wiwi da hodar ibilis da na kara kuzari da methamphetamine and ecstasy da sauransu, wadanda ke da alaka da laifuffuka 5,914.

Wani rahoto daga ofishin yaki da muggan kwayoyi da laifuffuka na MDD, ya ce a bara, an samu raguwar sarrafawa da bukatar kwayar Opium yayin da kasuwar magunguna ta yankin ke kara fadada.

A bara, Myanmar ta kona nau’ika 62 na muggan kwayoyi tare da lalata sinadaran hada su da darajarsu ta kai sama da dala milyan 667.91 a biranen Yangon da Mandalay da Taunggyi. (Faeza Mustapha)