logo

HAUSA

Kasar Sin za ta kara zuba jari a fannin muhallin halittu

2022-06-27 13:43:57 CMG Hausa

Ma’aikatar kula da muhalli ta kasar Sin, ta yi kira da a kara kaimi wajen zuba jari a fannin nazarin halittu da muhalli a daidai a gabar da ake kokarin daidaita tattalin arzikin kasar.

Dangane da ayyukan muhalli da aka zayyana a cikin manyan ayyuka 102 na kasar da ake fatan aiwatarwa a cikin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14 (2021-2025), ma'aikatar ta jaddada bukatar hanzarta ci gaban ayyukan da suka shafi ingancin iska, da ruwa, da kasa, da kawar da gurbataccen shara, da makaman nukiliya da kuma kula da tsaron sinadarin da ake fitarwa.

Zhang Jianhong na kungiyar raya tattalin arziki ta kasar Sin ya bayyana cewa, tanade-tanade kan aikin gine-gine na da muhimmanci wajen ba da jagoranci ga harkokin zuba jari, da daidaita samar da kayayyaki da bukatu yadda ya kamata, da warware muhimman matsalolin muhallin halittu, da sa kaimi ga yayata samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba.

Masu kula da harkokin masana'antu sun yi nuni da cewa, kasar Sin za ta mai da hankali kan bunkasa ci gaba da zuba jari a fannin gina kayayyakin more rayuwa a fannin kiyaye muhalli, da fadada hanyoyin samun kudade da zuba jari a bangaren zamantakewa. (Ibrahim Yaya)