logo

HAUSA

An bude taron G7 duk da zanga-zangar da ake yi

2022-06-27 11:08:58 CMG Hausa

 

An bude taron yini 3 na kasashen G7 masu karfin tattalin arziki, yayin da daruruwan mutane ke ci gaba da zanga-zanga. Dubban mutane ne suka fantsama kan titi suna zanga-zanga a birnin Munich na Bavara, a jajibirin taron da aka bude jiya Lahadi.

Masu zanga-zangar sun bukaci kasashen G7 su cika alkawarin da suka dauka, su kuma kara tashi tsaye wajen tinkarar matsalar sauyin yanayi da yunwa da sauran matsalolin da ake fama da su a duniya.

An ga ‘yan sanda da dama a wurin zanga-zangar. Kimanin ‘yan sanda 18,000 aka baza a fadin birnin Munich da kuma wurin da taron ke gudana.

Da take zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, wata mazauniyar garin mai suna Lisa Gaetner, ta yi korafi game da hauhawar farashin kayayyaki tana mai cewa, mutane suna kara shiga halin rashin kudi.

Ta ce ya kamata kasashen su rage kudin da suke kashewa kan ayyukan soji, su kara kokarin shawo kan matsalar sauyin yanayi. (Fa’iza Mutaspha)