logo

HAUSA

Yawan kwararru masana kimiyya da fasaha na kasar Sin ya karu zuwa miliyan 112 da dubu 341

2022-06-27 13:57:06 CMG Hausa

Kwalejin nazarin tsare-tsare na hukumar kula da harkokin kimiyya da fasaha ta kasar Sin, ya gabatar da rahoton nazarin albarkatun kwararru a fannin kimiyya da fasaha na kasar Sin na shekarar 2020, inda aka bayyana cewa, Sin ce ke da albarkatun kwararru a fannin kimiyya da fasaha mafi yawa a duniya.

Rahoton wanda aka gabatar yayin taron tattaunawa tsakanin masanan kimiyya da fasaha na kasar Sin karo na 24 da ya gudana a ranar 25 ga wata, ya kara da cewa, ya zuwa karshen shekarar 2020, yawan kwararru a fannin kimiyya da fasaha a kasar Sin ya karu zuwa miliyan 112 da dubu 341. Hakazalika a cikin shekaru kimanin 10 da suka gabata, matasa sun fi yawa a cikin adadin masanan kimiyya da fasaha na Sin, inda yawan ’yan kasa da shekaru 39 da haihuwa, ya kai kashi uku cikin hudu bisa adadin kwararrun. Kana yawan kwararru mata ma ya karu sosai. (Zainab)