logo

HAUSA

Shugaban Amurka ya sanya hannu kan dokar tsaron unguwanni don shawo kan matsalar bindiga

2022-06-26 17:59:29 CMG Hausa

Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya sanya hannu kan wani shirin doka na tsaron unguwannin kasar a fadar White House jiya Asabar, a wani kokari na shawo kan matsalar yawaitar bindigogi.

An zartas da shirin dokar tuni a wannan mako a majalisun dattawa da na wakilan Amurka, inda aka tanadi kara binciken masu shekaru 18 zuwa 21 da suka sayi bindigogi, da yanke hukunci mai tsanani kan mutanen da suka sayi bindiga ba bisa doka ba, da ware kudade don goyon-bayan ayyukan rigakafin yawaitar bindigogi a kasar.

Kwanan nan ne aka kara samun harbe-harben bindigogi a kasar Amurka, al’amuran da suka janyo hasarar rayuka da dama.

Sakamakon matsin lambar da aka yi musu, ‘yan siyasar Amurka da suka dade suna jan kafa wajen daidaita wannan matsala, sun yi shawarwari da cimma matsaya kan kafa dokar tabbatar da tsaron bindigogi. Duk da cewa wasu ‘yan siyasa da kafafen yada labaran Amurka sun bayyana shirin dokar a matsayin babban ci gaba na farko da gwamnatin tarayya ta samu a fannin tabbatar da tsaron bindiga a kusan shekaru 30 da suka gabata, amma, wasu masanan kasar sun nuna cewa, jam’iyyun siyasar kasar biyu, wato Democrat da Republican, sun cimma matsaya ne kawai a wasu fannoni kalilan. (Murtala Zhang)