logo

HAUSA

BRICS ta fitar da sanarwar Beijing da ta yi alkawarin kare tsaro da zaman lafiya a duniya

2022-06-24 17:05:35 CMG Hausa

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da ta fitar yayin taron kolinta na 14, kungiyar kasashen BRICS, ta yi alkawarin kare zaman lafiya da tsaro a duniya.

Haka kuma, yayin taron tattalin arziki da kasuwanci na kungiyar, an fitar da shirin raya harkokin kasuwanci a kasashen BRICS na Beijing, da nufin karfafa hadin gwiwa da inganta farfadowar tattalin arzikin duniya. (Fa’iza Mustapha)