logo

HAUSA

Amurka Za Ta Yi Amai Ta Lashe Game Da Dokar Dake Shafar Yankin Xinjiang Da Ta Zartar

2022-06-22 12:25:47 CMG HAUSA

 

Amurka ta fara amfani da dokar da ta zartar, na wai “Dokar Hana Aikin Tilas Ga Al’ummar Uygur” a jiya Talata. Wannan daftarin doka mai cike da karairayi na ikirarin hana shigar da kayayyakin yankin Xinjiang cikin kasar Amurka, sai dai an ba da ainihin shaidun dake tabbatar da cewa, babu aikin tilas a lokacin da ake samar da su.

Duk abin da Amurka ta fadi game da aikin tilas a jihar Xinjiang karya ce, mataki ne kawai da ta dauka domin yaki da kasar Sin. A hakika, ’yan siyasar Amurka sun nuna hali-ko-in-kula game da yanayin samun aikin yi a yankin, kuma yunkurinsu shi ne, shafawa kasar Sin bakin fenti da fakewa da batun hakkin Bil Adam. A sa’i daya kuma, da dakile fifikon da Xinjiang ke da shi wajen samar da kayayyaki, har ma da ware yankin daga tsarin samar da kayayyaki a duniya.

Manazarta na ganin cewa, kaddamar da wannan doka mai cike da yaudara, zai keta zaman oda da dokar cinikayya ta duniya, da kawo cikas ga dorewar samar da isassun kayayyakin da ake bukata a duniya. Ban da wannan kuma, watakila lamarin zai kawo cikas ga wasu kamfanonin Xinjiang dake fitar da kayayyaki zuwa ketare, amma Amurka ba za ta cimma burinta na hana bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ba. Kasuwanni mafi girma da Sin take da su da manyan bukatun duniya, za su goyi bayan kamfanonin Xinjiang, haka kuma ba za su rasa karfinsu na takara ba ko kadan, idan Amurka ta rufe kofarta.

A nata bangare, Amurka za ta yi amai ta lashe wajen amfani da wannan doka. Amurkawa masu sayayya ne za su dandana mummmuna tasirin dokar. A halin yanzu, Amurkawa na fuskantar hauhawar farashin kayayyaki mafi tsanani da aka gani cikin shekaru 40 da suka gabata. Bisa rahoton da manazarcin kamfanin Moody ya bayar, an ce, yawan kudin da ko wane iyalin Amurka ke kashewa a kowane wata, ya karu da dala 460 idan aka kwatanta da sauran shekarun da suka gabata.

Kamata ya yi, Sin ta dauki mataki mai karfi don kiyaye moriyar da ta dace da kamfanoni da al’ummarta, da kuma kiyaye dorewar tsarin samar da kayayyaki a duniya. Ita kuma Amurka dake gabatar da karairayi, za ta girbi abin da ta shuka. (Amina Xu)