logo

HAUSA

Wakilin Sin A MDD Ya Yi Kira Da A Mai Da Hankali Kan Batun Keta Hakkin Mata Da Yara Mata ‘Yan Asalin Amurka Da Canada Da Australiya

2022-06-21 11:13:19 CMG HAUSA

Jiya Litinin, wakilin Sin a MDD ya tattauna da mai daukar rahoto na musamman kan matsalar nuna karfin tuwo da keta hakkin mata a wajen taro karo na 50 na majalisar kare hakkin Bil Adama ta MDD, inda ya yi kira ga majalisar da ta maida hankali kan batun keta hakkin mata da yara mata ‘yan asalin kasashen Amurka da Canada da Australiya.

Wakilin Sin ya nuna cewa, wannan mai daukar rahoto na musamman ya gabatarwa majalisar wani rahoto dake nuna cewa, an nuna karfin tuwo kan mata ‘yan asalin kasar Amurka wadanda suka halarci harkokin siyasa, kuma wadannan mata da ‘yan mata da suke neman taimakon shari’a ne fuskantar matsaloli, ban da wannan kuma a Australiya, ‘yan asalin kasar ne suka dau wani babban kaso na matan da ake daure a gidan kurkuku, a Canada kuma, an yi wa ‘yan asalin kasar kisan kare dangi. Sin ta nuna matukar damuwa kan hakan.

Wakilin Sin ya nuna cewa, Sin na kalubalantar wadannan kasashe da su dubi laifufukan da suka aikata da daukar matakan da suka dace don kawar da nuna bambanci da ma karfin tuwo ga mata da yara mata ‘yan asalin kasashen, da kuma yin bincike mai zurfi kan irin wadannan laifuffuka don gurfanar da masu aikata laifi a gaban kotu, da samarwa mutanen da lamarin ya shafa taimakon kudi tare da biyansu diyya. (Amina Xu)