logo

HAUSA

An sake bude tashar jirgin kasa ta Fengtai dake Beijing bayan aikin fadada ta

2022-06-20 13:40:49 CMG HAUSA

 

An sake bude tashar jirgin kasa ta Fengtai ta birnin Beijing, wacce ta kasance tashar jirgin kasa ta kasar Sin mafi dadewa, kuma mafi girma a nahiyar Asiya, a yau 20 ga watan Yuni tashar ta soma aiki tun bayan ayyukan gyare-gyaren da aka gudanar a tashar na tsawon shekaru hudu.

Bayan sake budewar, tashar za ta kasance a matsayin wata babbar mahadar layukan dogo na kasar Sin, kamar hada layin dogo na hanyar jirgin kasa mai matukar sauri na Beijing zuwa Guangzhou, da Beijing zuwa Kowloon, kamar yadda babban kamfanin kula da sufurin layin dogo na kasar Sin ya bayyana, hukumar kula da sufurin jirgin kasan ta kara da cewa, za ta fara ne da gudanar da ayyukan hidimar zirga-zirgar jiragen kasa 120 a matakin farko.

An fara aikin gina tashar jirgin kasa ta Fengtai a shekarar 1895 a kudancin birnin Beijing. Tashar ta ci gaba da gudanar da ayyukan hidimar fasinjoji har zuwa shekarar 2010 a lokacin da aka rufe ta.

Tashar da aka gina, tana da girman murabbi’in mita kusan 400,000, da kuma hanyoyin layin dogo 32, da rumfunan jiran jiragen kasa 32. Tashar tana da girman daukar fasinjoji a kalla 14,000 a cikin kowace sa’a guda. Ita ce tashar jirgin kasa irinta ta farko a kasar Sin wacce ta hada dukkan tsarukan hidimar jiragen kasa wanda ya kunshi na jiragen kasa masu matukar sauri da kuma na jiragen kasan da aka saba gudanarwa da kuma jirgin kasa dake tafiya a karkashin kasa. (Ahmad)