logo

HAUSA

JKS Na Muhawara Kan Rahoton Gyaran Cibiyoyin Hada-hadar Kudi

2022-06-18 20:30:52 CMG Hausa

Sakatare Janar na kwamitin tsakiya na JKS, Xi Jinping, ya jagoranci taron ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin tsakiyar, game da muhawara kan rahoton gyara matsalolin da aka gano yayin da ake binciken ayyukan cibiyoyin hada-hadar kudi.

Taron na jiya ya bayyana cewa, kwamitin tsakiyar karkashin shugabancin Xi Jinping, na ba da muhimmanci sosai ga binciken, kuma yana daukar aikin a matsayin mai muhimmanci dake inganta sauyi a jam’iyyar da nuna cikakken jagorancinta. (Fa’iza Mustapha)