logo

HAUSA

Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi Ga Taron Tattalin Arzikin Duniya Na St. Petersburg

2022-06-18 16:24:24 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarta tare da gabatar da jawabi ga taron tattalin arzikin duniya karo na 25 da aka yi a St. Petersburg.

Xi Jinping, wanda ya halarci taron ta kafar bidiyo bisa gayyatar da aka yi, ya ce duniya na fuskantar muhimman sauye-sauye da annoba da ba a taba gani ba cikin karni, kana dunkulewar tattalin arzikin duniya ya gamu da tsaiko, baya ga kalubalen da ake fuskanta wajen aiwatar da muradun ci gaba masu dorewa da MDD ke son cimmawa zuwa shekarar 2030.

Ya ce a lokacin da duniya ke da burin samun ci gaba mai dorewa cikin daidaito, ya kamata a yi amfani da damarmakin dake akwai wajen tunkarar kalubalen da ake fuskanta da hada hannu wajen aiwatar da shirin ci gaban duniya domin gina al’umma mai kyakkyawar makoma da zaman lafiya.

Ya kara da cewa, da farko, akwai bukatar samar da kyakkyawan yanayin neman ci gaba. Na biyu, ya kamata a karfafa hadin gwiwa a fannin neman ci gaba. Na uku, a inganta dunkulewar tattalin arzikin duniya, sai na hudu, a ingiza neman ci gaba ta hanyar kirkire-kirkire.

Bugu da kari, shugaban na Sin ya ce tubalin tattalin arzikin kasarsa na juriya da karfi kuma mai dorewa cikin lokaci mai tsawo, bai sauya ba. kuma ana da kwarin gwiwa kan bunkasar tattalin arzikin kasar.

Har ila yau, shugaban na kasar Sin ya ce Sin za ta ci gaba da neman ci gaba mai inganci da fadada manufar bude kofa ga ketare da ingiza hadin gwiwa mai inganci kan shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”. (Fa’iza Mustapha)