logo

HAUSA

Yang Jiechi ya jagoranci taron wakilan BRICS kan harkokin tsaro karo na 12

2022-06-16 12:00:36 CMG Hausa

Yang Jiechi, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis mai mulki a kasar Sin(JKS), kana daraktan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin kolin JKS, ya jagoranci taron wakilan kungiyar BRICS kan harkokin tsaro karo na 12 ta kafar bidiyo a jiya Laraba a nan birnin Beijing, inda ya jaddada cewa, a ko da yaushe kasashen BRICS suna nacewa ga ruhin BRICS na "bude kofa, da yin hakuri, da hada gwiwa da samun nasara tare", kana suna kiyaye moriyar bai daya na dimbin kasashe masu tasowa, za kuma su bi tsarin siyasa na shugabannin kasashen kungiyar biyar, don yin shirye-shirye sosai a dukkan fannoni kan taron shugabannin BRICS karo na 14 mai zuwa.

Yang Jiechi ya jaddada cewa, kamata ya yi kasashen BRICS su bi tsarin zamani, don kara samar da zaman karko da kwarin gwiwa kan yanayin da duniya ke ciki. Dole ne su aiwatar da ra’ayin kasancewar bangarori da dama na gaskiya, da himmatuwa wajen samar da tsaro tare, da kuma tantance kalubalen gargajiya da wanda ba na gargajiya ba, don tabbatar da cikakken tsaro. Kuma ya kamata su yi kokari tare don cimma nasarar samar da tsaro na hadin gwiwa, sa’an nan su yi la’akari da batutuwan tsaro da na ci gaba da nufin tabbatar da tsaro mai dorewa.

Ban da wannan kuma, taron ya yi nazari kan ayyukan sashen yaki da ta'addanci da tsaron Intanet, kuma an amince da inganta tsare-tsaren da suka shafi hadin gwiwar yakar ayyukan ta'addanci, da na tsaron intanet na kasa da kasa, tare da kiyaye muhimmiyar rawar da Majalisar Dinkin Duniya ke takawa wajen daidaita harkokin yaki da ta'addanci na duniya, tare da yin kira da a kafa wani tsarin gudanar da harkokin intanet na duniya mai hade da bangarori daban daban da wakilci da kuma demokuradiyya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)