logo

HAUSA

An tsinci ‘yar makarantar Chibok shekaru 8 bayan BH ta yi garkuwa da ita

2022-06-16 09:40:58 CMG Hausa

             

An gano daya daga cikin ‘yan makarantar sakandare sama da 200 da mayakan Boko Haram suka sace a makarantarsu a jihar Borno, dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, shakaru takwas bayan kungiyar masu tsattsauran ra’ayin ta yi garkuwa da daliban, kamar yadda sojoji suka tabbatar.

Matar, mai suna Mary Ngoshe, an yi amanna tana daya daga cikin daliban Chibok 276 da kungiyar Boko Haram ta yi awon gaba da su, a ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014, a makarantar sakandaren ‘yan mata dake garin Chibok, a jihar Borno, an tsinci dalibar ne a lokacin da dakarun Najeriyar suke gudanar da ayyukan sintiri, kamar yadda wata sanarwar da sojojin suka fitar ta bayyana.

Sojojin runduna ta 26 ta Najeriya, sun yi nasarar ceto Ngoshe tare da danta, a lokacin da sojojin suka kaddamar da farmaki a wani gari dake kusa da inda Ngoshe take da zama, sanarwar ta kara da cewa, ana ci gaba da gudanar da binciken yanayin lafiyar matar. (Ahmad)