logo

HAUSA

Ya kamata kasar Birtaniya ta daina keta hakkin dan Adam

2022-06-14 19:58:59 CMG Hausa

Game da shirin da kasar Birtaniya ke yi mayar da masu neman mafaka dari daya zuwa kasar Ruwanda, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru a yau cewa, ya kamata kasar Birtaniya ta daina keta hakkin dan Adam, da daukar matakai don amsa sukan da ake mata a ciki da waje kan wannan batu.

Rahotanni na cewa, ma’aikatar harkokin cikin gidan kasaar Birtaniya ta sanar a kwanakin baya cewa, kasar tana shirin mika masu neman mafaka na kasashen waje da ba su samu iznin shiga kasar Birtaniya ba zuwa kasar Ruwanda, jirgin sama na farko dauke da mutane 100 zai tashi daga kasar Birtaniya a yau ranar 14 ga wata.

Game da wannan batu, Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, kasar Birtaniya ta kan kira kanta mai kare hakkin dan Adam, kuma ta kan zargi sauran kasashe kan batun kare hakkin dan Adam. Amma lokacin da kasar Birtaniya take fuskantar batun ‘yan gudun hijra da bakin haure, ta kan yi watsi da matakan kare hakkin dan Adam da ma ayyukan jin kai da ta saba tallatawa, ta kuma yi watsi da nauyin da ya rataya a bisa wuyenta, da kuma neman mika masu neman mafaka zuwa wasu kasashen waje don daidaita matsalar. (Zainab)