logo

HAUSA

An kaddamar da makon wayar da kai kan tsimin makamshi na 2022 a kasar Sin

2022-06-13 14:47:34 CMG Hausa

A yau Litinin aka kaddamar da makon tsimin makamashi na kasa na shekarar 2022 a kasar Sin. Wannan shi ne karo na 32 da makon na wayar da kan jama’a kan tsimin makamshi ya gudana a kasar. Taken makon na bana, wanda zai gudana daga yau 13 zuwa 19 ga wata, shi ne “ Kiyaye muhalli da rage fitar da sinadarin Carbon da tsimin makamashi”.

Da safiyar yau, hukumar kula da raya kasa da aiwatar da gyare-gyare ta kasar da gwamnatin birnin Beijing, suka kaddamar da makon na matakin kasa da birnin Beijing ta kafar intanet, wanda zai mayar da hankali kan shirye shiryen wayar da kai guda 7 da suka hada da: nuna nasarorin da kasar ta samu wajen tsimin makamashi, da ayyukan tsimin makamashi da rage fitar da sinadarin carbon a kamfanonin dake muhimman masana’antu. Da nuna nasarorin shirin kare muhalli da fasahar adana makamashi da kuma nune-nunen fasahohin tsimin makamshi mafi kyau. Akwai kuma shirye shiryen wayar da kai kan matakan tsimin makamashi da na wayar da kai kan kare gurbatar muhalli daga robobi domin gina muhalli mai kyau. Sai kuma shirye shiryen wayar da kan jama’a kan tsimin makamashi na Beijing.  (Fa’iza Musatapha)