logo

HAUSA

Sabuwar tawagar jami’an lafiya na kasar Sin ta isa Uganda

2022-06-13 11:13:49 CMG Hausa

Tawaga ta 22 ta jami’an lafiya Sinawa, ta isa Uganda domin gudanar da ayyukan dake da nufin bunkasa kiwon lafiya a kasar ta gabashin Afrika.

Guo Zhiping, shugaban tawagar, ya shaidawa Xinhua a jiya cewa, tawagar ta kunshi likitoci 7 dake da kwarewa a fannoni daban-daban da suka hada da lafiyar ciki da hanji da mafitsara da cututtuka masu yaduwa da lafiyar kunne da hanci da makogwaro da kula da marasa lafiya a dakin tiyata da sauransu.

A cewarsa, aikin tawagar ta 22 shi ne, amfani da kwarewarsu wajen kula da lafiyar al’ummar Uganda da ci gaba da zurfafa hadin gwiwa da shugabancin asibiti da bayar da horo da duba marasa lafiya ta hanyoyin sadarwar zamani da kiwon lafiyar al’umma.

Bugu da kari, ya ce suna sa ran a shekara mai zuwa, kwararru Sinawa a fannin lafiyar manya da na tiyata da kandagarki da dakile COVID-19 da sauran cututtuka masu yaduwa da na likitancin gargajiya na Sin, za su karawa juna sani tsakaninsu da takwarorinsu na Afrika. (Fa’iza Mustapha)