logo

HAUSA

Wang Yi ya gana da ministar harkokin wajen New Zealand Nanaia Mahuta ta kafar bidiyo

2022-06-13 21:21:47 CMG Hausa

 

Yau ne, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da takwararsa ta kasar New Zealand Nanaia Mahuta bisa bukatarta ta kafar bidiyo. Wang ya jaddada cewa, ya kamata kasashen Sin da New Zealand, su takaita nasarorin da suka cimma a cikin shekaru 50 da suka gabata, da kara amincewa da juna, da mai da hankali kan hadin gwiwar moriyar juna, da kara bude kofa nan da shekaru 50 masu uwa, da samun nasara cikin lumana a tsakaninsu

A nata jawabin kuwa Mahuta ta ce, kasar New Zealand ta kuduri aniyar bunkasa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu, da sa kaimi ga yin hadin gwiwa da mu'amalar al'adu a tsakaninsu a fannonin tattalin arziki, da kasuwanci da sauran fannoni. Kasar New Zealand ta dade tana martaba manufar “Sin daya tak a duniya”, ta kuma yaba da yadda kasar Sin take girmama sabuwar manufar harkokin wajenta mai cin gashin kai.

Wang ya ce, dangantakar dake tsakanin Sin da kasar New Zealand, wani misali ne mai nasara na samun nasara tare a hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tsarin zamantakewa daban-daban, da tarihi, da al'adu da kuma matakan ci gaba. Dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da New Zealand, ta haifar da sakamako masu tarin yawa, ta kuma taka muhimmiyar rawa a dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen da suka ci gaba.(Ibrahim)