logo

HAUSA

Xi Jinping ya yi rangadin aiki a lardin Sichuan

2022-06-12 15:44:01 CMG Hausa

Kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya je birnin Meishan na lardin Sichuan dake kudu maso yammancin kasar domin rangadin aiki.

Da farko, Xi ya je kauyen Yongfeng na garin Taihe na birnin, wanda ya mallaki gonaki kadada 431 da iyalai manoma 2133, domin binciken yadda kauyen yake ingiza gina gonaki masu inganci domin samun karin hatsi.

Wani jami’in kauyen ya gaya wa shugaba Xi cewa, matsakaicin kudin shigar kowanne manomin kauyen ya kai kudin Sin yuan dubu 28 a shekarar 2021, adadin da ya kai matsayi na hudu a fadin lardin Sichuan.

Hakika yayin taruka biyu na bana, shugaba Xi ya taba bayyana cewa, samar da isasshen abinci ga al’ummun kasa, shi ne aiki mafi muhimmanci ga gwamnatin kasar Sin, don haka ya bukaci a gina gonaki masu inganci kadada miliyan 66.7 a fadin kasar ta Sin. 

Daga baya shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi tattaki zuwa birnin Yibin, inda ya ziyarci mahadar wasu koguna uku, da kwalejin Yibin, gami da kamfanin kera kayan laturoni da na samar da wutar lantarki na Jimi, don kara fahimtar yadda ake gyarawa da kiyaye muhallin yankin kogin Yangtze, da samar da guraban ayyukan yi ga daliban da suka gama karatu a jami’a, da harkokin kirkire-kirkire na kamfanoni.

Mahadar kagunan uku ta hada da kogin Yangtze, da kogin Jinsha da na Min a birnin Yibin. Cibiyar wannan wurin na da tsawon kilomita 4.2, da fadin hekta kimanin 73.3, wadda ita ce muhimmin bangare na aikin kiyaye tsaftar muhallin halittu na kogin Yangzte a Yibin, inda ake samar da hidimomin yawon bude ido da al’adu da sauransu ga al’umma. (Jamila&Murtala)