logo

HAUSA

Ministan Tsaron Sin Ya Yi Magana Kan Hangen Nesan Kasar Sin Game Da Tsarin Yanki A Taron Tattaunawa Na Shangri-La Karo Na 19

2022-06-12 16:20:29 CMG Hausa

Yau ne, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan tsaron kasar Wei Fenghe, ya gabatar da jawabi kan ra'ayin kasar Sin, game da odar yankin a yayin taron tattaunawa na Shangri-La karo na 19 da aka gudanar a kasar Singapore.

Wei ya ce, babu mai iya dakushe ci gaban kasar Sin, yana mai cewa, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen neman ci gaba cikin lumana.

Ya kara da cewa, ci gaban kasar Sin ba barazana ba ce ga wasu. Sabanin haka, hakan wata babbar gudummawa ce ga zaman lafiya da ci gaban duniya baki daya. Ya ce kasar Sin tana nacewa kan manufar tsaron da ta dace da yanayin tsaro.

A game da tambayar da aka yi masa kan yankin Taiwan kuwa, Wei ya ce Taiwan wani bangare ne na kasar Sin, kuma batun Taiwan harkokin cikin gidan kasar Sin ne. Kuma babu shakka, duk masu neman 'yancin kai na Taiwan a kokarin raba kasar Sin, hakika zai zo karshe, haka kuma tsoma bakin kasashen waje ba zai taba yin nasara ba.

Ya ci gaba da cewa, sake hadewar Taiwan da babban yanki cikin lumana, shi ne babban fatan al'ummar Sinawa. Wei ya ce, duk wanda ya kuskura ya nemi tayar da batun ballewar yankin Taiwan daga kasar Sin, hakika ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen mayar da duk wani martani da ya dace, kuma za mu mayar da martani ko ta halin kaka. Ya kuma kara da cewa, bai kamata wani ya raina karfin da sojojin kasar Sin suke da shi na kare iko da cikakkun yankunanta ba. (Ibrahim)