logo

HAUSA

Dakarun tsaron hadin gwiwar kasashen tafkin Chadi sun kashe mayakan Boko Haram sama da 800 a shiyyar

2022-06-11 17:40:00 CMG Hausa

Sama da mayakan kungiyar masu tsattsauran ra’ayi ta Boko Haram 800 aka kashe a samamme na baya bayan nan da dakarun tsaron hadin gwiwa na shiyya (MNJTF) suka kaddamar a yankunan tafkin Chadi, kamar yadda kwamandan rundunar ya bayyana.

Manjo janar Abdul Kalifa Ibrahim, kwamandan rundunar MNJTF yace, aikin samamen wanda aka yiwa taken “zaman lafiyar tafki," an shafe kwanaki 75 ana gudanar da shi, wanda ya kumshi dakarun tsaron kasashen Kamaru, Najeriya, Chadi, da jamhuriyar Nijer.

Yace, rundunar tsaron MNJTF ta gudanar da ayyukan ne ta hanyar girke dakarun sojoji na kasa da na ruwa, inda suka yi yiwa ‘yan ta’addan matsin lamba, tare da kaddamar da hare kan babbar maboyarsu, inda suka yi musu kawanye suka hana su sukuni.

Ita dai rundunar tsaron MNJTF, runduna ce da kasashen Kamaru, da Chadi, da Nijer, da Najeriya, da kuma Benin suka kafa, a kokarin yakar kungiyar Boko Haram, da ta ISWAP, wadanda ke barazana ga zaman lafiyar wadannan kasashe har ma da shiyyar baki daya.(Ahmad)