logo

HAUSA

Ministan wajen Sin ya tattauna da shugaban babban taron MDD

2022-06-11 17:42:36 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, a ranar Juma’a, ya tattauna ta wayar tarho da shugaban babban taron MDD karo na 76, Abdulla Shahid.

Wang ya bayyana cewa, wannan sabon zagaye na taron MDDr ya samar da sabon yanayin da zai inganta tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa, da inganta hadin kai a tsakanin mambobin kasashen duniya, kana ya bayar da sabbin gudunmawa ga zaman lafiya da cigaban duniya.

Wang ya bukaci babban taron MDDr da ya kiyaye tsarin dokokin MDD, da aiwatar da hakikanin hadin gwiwar bangarori daban-daban, kana ya taka muhimmiyar rawa da kuma bayar da karin gudunmawa a wasu bangarorin, kamar bangaren yaki da sauyin yanayi, da yaki da annobar COVID-19, da kokarin neman cigaba mai dorewa, wadanda suke da matukar muhimmanci ga makomar al’ummun kasa da kasa.

A nasa bangaren, Shahid ya ce, yana matukar yabawa muhimmin kokarin da kasar Sin ke yi, da kuma gaggarumar gudunmawar da take bayarwa ga ayyukan babban taron MDD, kana ya yabawa kasar Sin bisa taimakon da take ba shi wajen gudanar da ayyukansa.

Shahid yace, zai cigaba da karfafa yin aiki tare da kasar Sin, tare da karfafa hadin gwiwa don warware kalubalolin dake shafar kasa da kasa, da aiwatar da hadin gwiwar bangarori daban-daban, da kiyaye ikon gudanarwar MDD, da kuma daga matsayin ayyukan farfado da cigaban duniya bayan kawo karshen annoba.(Ahmad)