logo

HAUSA

Sin Na Da Karfin Zuciya Da Kwarewa Wajen Tabbatar Da Bunkasar Cinikin Waje Ba Tare Da Tangarda Ba

2022-06-09 14:53:56 CMG HAUSA

Bisa yadda kasar Sin ta raya harkokin ciniki da kasashen waje ba tare da tangarda ba a bana, daga watan Janairu zuwa watan Afrilun bana, jimillar kudin da ta samu daga harkokin shige da fice ta kai kudin Sin RMB yuan triliyan 12.58, wadda ta karu da kashi 7.9 cikin 100 bisa makamancin lokaci na bara. Idan aka kwatanta da kungiyar tarayyar Turai, da kasashen Japan da Birtaniya, kasar Sin ta fi samun karuwar cinikin waje.

Wang Shouwen, mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin kuma mataimakin wakilin kasar Sin mai kula da shawarwarin ciniki tsakanin kasa da kasa ya bayyana jiya Laraba cewa, kasar na da karfin zuciya da kwarewa wajen tabbatar da bunkasar cinikin waje mai inganci ba tare da tangarda ba.

Wang Shouwen ya kara da cewa, nan gaba ma’aikatar kasuwanci ta kasar za ta rubanya kokarinta na biyan bukatun kamfanonin dake ciniki da kasashen waje, a kokarin tabbatar da ganin, sun samu isassun kwangiloli, fadadar kasuwa, da samun kwanciyar hankali a masana’antunsu. Haka kuma, yayin da ma’aikatar take goyon bayan bunkasar ciniki, za ta kuma mai da hankali kan sabunta harkokin cinikin. (Tasallah Yuan)