logo

HAUSA

Kasar Sin tana goyon bayan a sake fasalin WTO bisa hanyar da ta dace

2022-06-09 22:00:55 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin Shu Jueting, ta bayyana a yau Alhamis cewa, ministan harkokin cinikayya na kasar Sin Wang Wentao, zai halarci taron ministoci na kungiyar cinkayya ta duniya(WTO) karo na 12, da zai gudana a birnin Geneva daga ranar 12 zuwa 15 ga wata.

Shu ta shaidawa taron menama labarai cewa, a cikin 'yan shekarun baya-bayan nan, dunkulewar tattalin arzikin duniya ta ci karo da babban kalubale, a yayin da nuna ra’ayi na kashin kai da kariyar cinikayya ke karuwa, lamarin da ke kawo cikas ga iko da ingancin kungiyar ta WTO

Shu Jueting ta kara da cewa, dukkan mambobi suna fatan ganin kungiyar WTO ta dawo da ayyukanta na yau da kullum da kuma ciyar da dokokinta gaba don tafiya daidai da zamani.

Kakakin ya kara da cewa, kasar Sin za ta himmatu wajen ganin an inganta yin gyare-gyare a kungiyar bisa hanyar da ta dace, da kuma goyon bayan raya tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban, da kuma halastattun hakkoki da muradun kasashe masu tasowa mambobin kungiyar.