logo

HAUSA

Boris Johnson ya yi nasara a kuri’ar yanke kauna da mambobin jam’iyyarsa suka kada kan makomar mulkinsa

2022-06-07 11:14:29 CMG Hausa

 

Firaministan Birtaniya, Boris Johnson ya yi nasara a kuri’ar yanke kauna kan jagorancinsa da mambobin majalisar kasar na jam’iyyar Conservative suka kada a jiya Litinin.

Boris Johnson ya samu kuri’un goyon baya 211 daga cikin mambobi 359, adadin da ya dara kuri’u 180 da yake bukata na samun rinjaye.

Bisa ka’idojin da ake amfani da su yanzu, Boris Johnson ba zai sake fuskantar wata kuri’ar yanke kauna kan makomar jagorancinsa ba har na tsawon shekara guda, saboda nasarar da ya samu a jiya.

Firaministan ya shafe watanni yana fama da badakalar halartar liyafa tare da ma’aikatansa a fadar Downing Street, yayin da ake kullen dakile yaduwar COVID-19 a shekarar 2020 da 2021. ’Yan sandan Birtaniya sun ci shi tara a watan Afrilu saboda halartar liyafar, lamarin da ya sa shi zama Firaminista mai ci na farko a tarihin Birtaniya da aka ci tara saboda karya doka. (Fa’iza Mustapha)