logo

HAUSA

Sin: Yadda ake samun matsakacin harbe-harben bindiga 1.5 a kowace rana a Amurka abin mamaki ne

2022-06-07 21:06:12 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya shaidawa taron manema labaru da aka saba yi Talatar nan cewa, kididdigar shafin yanar gizo kan matsalar harbe-harben bindiga ta Amurka ta nuna cewa, an samu harbe-harbe guda 246 da kowanensu ya haddasa mutuwar mutane fiye da 4 ko jikkata wasu da dama da aka yi a Amurka a shekarar 2022 da muke ciki, inda ya kai matsakaicin 1.5 a kowace rana. Ya kuma ce, wannan adadi abin mamaki ne, domin ba adadi ne kawai ba, har ma yana wakiltar rayukan da ba sa kirguwa da aka yi hasara da ma raba iyalai.

Ranar 3 ga watan Yuni, ita ce ranar wayar da kan jama'a game da harbe-harben bindiga a kasar  Amurka. Jama’a ko ina a fadin Amurka, sun shirya ayyuka don nuna juyayi ga wadanda rikicin harbin bindiga ya rutsa da su, tare da yin kira ga gwamnatin Amurkar, da ta dauki matakin kawo sauyi da kuma hana aukuwar matsalar harbin bindiga a kasar