logo

HAUSA

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin: Amurka ce sanadin matsalolin abinci a duniya

2022-06-06 21:27:48 CMG Hausa

Zhao Lijian, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya bayyana a wajen taron manema labarai da ya gudana a yau Litinin cewa, kasar Amurka ce ta haifar da dukkan matsalolin abinci da duniya ta fuskanta a lokutan baya. A yanayin da ake ciki a halin yanzu, ya kamata al’ummun kasa da kasa su yi aiki tare, wajen tabbatar da zaman lafiya, da shirya tattaunawa, da samar da kyakkyawan yanayin da zai taimaka wajen warware matsalolin abinci da duniyar ke fuskanta. Ruruta wuta, da sanya takunkumai ba tare da kakkautawa ba, hakan ba zai taimaka wajen daidaita yanayin da ake ciki a shiyya ba, sai dai ma ya kara ta’azzara matsalar abincin da ake fama da ita.  

A baya bayan nan, shugaban kasar Senegal, kana shugaban karba-karba na kungiyar tarayyar Afrika AU, ya ce takunkuman da kasashen yammacin duniya ke kakabawa Rasha sun yi matukar shafar yanayin samar da abinci a Afrika. Shirin samar da abinci na MDD a kwanan nan yayi gargadin cewa, mai yiwuwa ne bil adama ya fuskanci matsalar karancin abinci mafi muni da ba a taba gani ba tun bayan yakin duniya na II.

A yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai dangane da wannan, Zhao Lijian ya bayyana cewa, “A hakika dai, kasar Amurka ce sanadin  matsalolin abincin da duniya ta fuskanta a lokutan baya. Kasar Amurka da wasu tsirarrun kasashe suke rike tsarin cinikayyar abinci ta duniya, sun kafa wani tsarin ‘babakere a fannin abinci', sun lahanta yanayin farashin abinci a kasa da kasa, kuma suna cigaba da samun kazamar riba ta hanyar tsawwala farashin abincin da haifar da mummunan karancin abincin a duniya. Yayin da kasar Amurkar ke zargin wasu kasashe da tara hatsi, tana kuma umartar wasu kasashen da su bude ma’ajiyar abincinsu kuma su fitar da hatsin, kasar bata taba rage yawan hatsin da take amfani da su wajen samar da makamashi. A lokaci guda kuma, tana amfanin da wannan damar wajen tsawwala farashin hatsi domin cimma wata moriya ta kashin kai. Wannan halayyar rashin kirki ne.”(Ahmad)