logo

HAUSA

Rasha zata daina samar da iskar gas ga kamfanonin Demark da Jamus

2022-06-01 11:54:37 CMG Hausa

Jiya Talata, katafaren kamfanin makamashi na kasar Rasha Gazprom, ya ce zai daina samar da iskar gas ga Orsted, kamfanin samar da gas mafi girma na kasar Denmark. Haka kuma, zai daina samarwa Jamus gas din da yake samarwa karkashin yarjejeniyarsu da kamfanin makamashi na Shell Energy Europe.

Dukkan kamfanonin Orsted da Shell Energy Europe, sun shaidawa Gazprom cewa ba za su rika biyan kudin gas da takardar kudin rubles na Rasha ba.

Don haka, matakin na dakatar da samar da iskar gas din zai fara aiki ne daga yau Laraba.

Shugaban Rasha Vladimir Putin, ya rattaba hannu kan wani umarni a ranar 31 ga watan Maris din bana, game da sabbin ka’idojin cinikayyar iskar gas da kasashen da ba kawayen Rasha ba. Umarnin, ya yi tanadin cewa, Rasha za ta dakatar da duk wata yarjejeniya idan kasashen suka ki biyanta da takardar kudin rubles. (Fa’iza Mustapha)