logo

HAUSA

Sin: Ya Fi Kyau Amurka Ta Kula Da Harkokinta A Maimakon Koyar da wasu Kasashe Darasi

2022-05-31 20:34:48 CMG HAUSA

Ranar 31 ga watan nan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya sake musunta jawabin sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken, dangane da manufar Amurka kan kasar Sin. Zhao Lijian ya bukaci Amurka da ta kalli yadda take keta hakkin dan Adam a gida, ta dakatar da koyawa sauran kasashe darasi, ta kula da harkokinta yadda ya kamata. 

Dangane da kalaman Blinken, masu nasaba da batutuwan Xinjiang, da Tibet, da Hong Kong, Zhao Lijian ya ce, Amurka na yunkurin dora wa kasar Sin laifi, wanda alal hakika laifin Amurkan ne da ba za ta iya musuntawa ba. Ya ce wajibi ne Amurka ta mutunta ikon mulkin kasar Sin, da muradun kasar Sin ta fuskar tsaro da bunkasuwa, ta dakatar da bata sunan kasar Sin ta hanyoyin kirkiro, da baza jita-jita da karairayi, haka kuma ta daina tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin, bisa hujjar batun hakkin dan Adam. (Tasallah Yuan)