logo

HAUSA

Rokar Long March-5 Ta Isa Cibiyar Harba Kumbo

2022-05-30 11:25:22 CMG HAUSA

Rokar dakon kumbo ta Long March-5B Y3, ta isa cibiyar harba kumbuna ta kasar Sin dake lardin Hainan a jiya Lahadi. Za a yi amfani da rokar ne wajen harba kumbon dakin gwaji na Wentian zuwa cibiyar binciken sararin samaniya ta kasar Sin.

Hukumar kula da kumbuna ta kasar Sin, ta ce an riga an kai rokar, tare da kumbon dakin gwaji na Wentian, cibiyar harba kumbuna ta Wenchang, inda a nan za a harhada tare da gwada su.

Hukumar ta ce ana shirya dukkan kayayyakin da ake bukata wajen gudanar da aikin a cibiyar harba kumbuna.

An tsara cewa, za a harba kumbon dakin gwaji na Wentian inda zai hade da babban bangaren tashar sararin samaniya ta Tianhe a watan Yuli, kana kumbon dakin gwaji na Mengtian, zai hadu da tashar Tianhe a cikin watan Oktoba, domin kammala ginin tashar sararin samaniyar ta kasar Sin yayin da yake cikin falaki.

Idan aka kamala aikin, za a samu tashar binciken sararin samaniya mai siffar T.  (Fa’iza Mustapha)