logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya gabatar da jawabi a rubuce ga taron ministocin harkokin wajen Sin da kasashe tsibiran tekun Pasifik

2022-05-30 14:39:01 CMG Hausa

A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi a rubuce ga taron ministocin harkokin wajen Sin da kasashe tsibiran tekun Pasifik karo na biyu.

A jawabin da ya gabatar, shugaba Xi ya jaddada cewa, kullum kasar Sin na nacewa ga kiyaye zaman daidaito a tsakanin kasashe manya da kanana, kuma tana bunkasa huldar da ke tsakaninta da kasashe tsibiran tekun Pasifik bisa manufar zaman adalci da cin moriyar juna da rikon gaskiya. Duk da sauye-sauyen da duniya ke fuskanta, kasar Sin za ta kasance aminiya ta kut da kut ga kasashe tsibiran tekun Pasifik.(Lubabatu)