logo

HAUSA

Tsarin Kasar Sin Na Bincike Da Sa Ido Kan Harkokin Kudi Ya Ba Da Tabbaci Kan Bunkasar Kasa Mai Inganci

2022-05-29 16:17:20 CMG HAUSA

A cikin shekaru 10 da suka wuce, tsarin bincike da sa ido kan harkokin kudi ya taka muhimmiyar rawa cikin tsare-tsaren sa ido na kasar Sin, wanda ya ba da tabbaci kan bunkasar kasar Sin mai inganci. An samu sakamako mai kyau a fannin binciken harkokin tattalin arzikin kasar cikin shekaru 10 da suka wuce. Aikin binciken harkokin kudi ya kara azama kan kyautata tsare-tsare fiye da dubu 70, tare da mika wa hukumomin aiwatar da doka da hukumomin sa ido da ladabtarwa bayanai fiye da dubu 60 dangane da wasu batutuwa.

A cikin tsarin kasar Sin na binciken harkokin kudi, an mayar da aikin binciken harkokin kudi a gaban kome. Yayin da hukumomin binciken harkokin kudi suke sa kaimi kan zurfafa gyare-gyare da ake yi a fannin tsarin harkar kudi, sun kara yin bincike kan aiwatar da kasafin kudi da daftarin lissafi na karshe. Haka kuma, hukumomin binciken harkokin kudi sun rika sa ido don ganin an yi amfani da kudi yadda ya kamata, a kokarin kyautata aiwatar da manufar harkar kudi, sun kuma kara azama kan ware kudi kan lokaci, da tsara amfani da kudin daidai yadda ake bukata.

A cikin shekaru 10 da suka wuce, hukumomin binciken harkokin kudi na kasar Sin suna ta kara karfin bincike a fannonin lafiya, da kula da tsoffi, samar da aikin yi, da samar da wuraren kwana, da aikin gona, da raya yankunan karkara, da ma sauran fannonin zaman rayuwar jama’a. (Tasallah Yuan)