logo

HAUSA

Jagororin JKS sun tattauna kan ka'idojin aikin shawarwarin siyasa na jam'iyyar

2022-05-27 21:13:42 CMG Hausa

Yau ne, babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jagoranci taron hukumar siyasa na kwamitin kolin, don tattauna wata ka'ida game da ayyukan jam'iyyar da ta shafi harkokin shawarwarin siyasa.

Taron ya kuma bayyana cewa, shawarwarin siyasa wani muhimmin bangare ne na tsarin hadin gwiwa tsakanin jam'iyyun siyasa wanda JKS dake ke jagoranta, kuma wani babban nau'i ne na tsarin tuntuba na demokuradiyya mai salon gurguzu.

Haka kuma, shawarwarin siyasa wata muhimmiyar hanya ce ta hada hikima, da cimma daidaito, da yanke shawara na kimiyya da demokuradiyya

A cewar taron, ka'idar tana da matukar muhimmanci wajen karfafa shugabancin jam'iyyar JKS a kan ayyukan shawarwarin siyasa, da kyautata ayyuka, da kiyayewa da inganta sabon tsarin jam'iyyar siyasa na kasar, da karfafa tare da raya hadin kan 'yan kishin kasa.