logo

HAUSA

Zhang Jun ya soki Amurka game da gazawarta na daidaita batun takunkuman da aka kakabawa Sudan ta kudu

2022-05-27 11:29:59 CMG Hausa

Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun ya soki kasar Amurka, bisa gazawarta na daidaita batun takunkuman da aka kakabawa kasar Sudan ta kudu.

Zhang Jun ya ce, Amurka ta gaza sauke nauyin dake wuyanta, a matsayinta na mai gabatar da kuduri a kwamitin tsaron MDD, kan batun dake da nasaba da takunkumai kan Sudan ta kudu.

Jami’in ya ce nauyi ne a wuyan kasa mai kujerar dindindin a kwamitin tsaro, ta gabatar da gamsasshen bayanin yadda za a cimma matsaya, maimakon kafewa kan nata ra’ayi na kashin kai.

Kasashe da dama mambobin kwamitin tsaron MDD, ciki har da na nahiyar Afirka, sun nuna rashin gamsuwa game da kudurin da aka gabatar. To sai dai kuma Amurka ta ci gaba da nacewa, wajen tabbatar da matsayarta, game da kudurin da bai samu goyon bayan sauran sassa ba. Don haka ne ma, kasar Sin ta yanke shawarar kin jefa kuri’ar ta.

Su ma kasashen Gabon, da India, da Kenya, da Rasha sun kauracewa kada kuri’unsu a kudurin na jiya Alhamis, wanda ke kunshe da sabunta kakabawa Sudan ta kudu takunkumi.

A jiya Alhamis ne kwamitin tsaron MDD ya amince da kuduri mai lamba 2633, wanda ya tanaji tsawaita takunkumin hana Sudan ta kudu sayen makamai, da sauran takunkuman da suka shafi kasar, har zuwa ranar 31 ga watan Mayun shekara mai zuwa. (Saminu)