logo

HAUSA

Kasar Sin ta ce Blinken ya yada bayanan karya a cikin jawabinsa

2022-05-27 21:01:33 CMG Hausa

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fada Juma'ar nan cewa, jawabin da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yi kan manufofin kasar Sin, ya yada labaran karya a cikinsa, ya kuma azuzuta wai "barazanar kasar Sin", da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin da kuma bata sunan manufofin cikin gida da waje na kasar Sin.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya shaidawa taron manema labarai cewa, kasar Sin ta nuna rashin amincewarta da ma adawa da kakkausar murya kan wannan jawabi.

Wang ya kara da cewa, sakatare Blinken ya bayyana cewa, Amurka ba za ta nemi rikici ko tayar da wani sabon yakin cacar baka da kasar Sin ba, kuma tana son zama lafiya da kasar Sin, za mu jira mu gani.

Ya kuma lura da cewa, Amurka tana ikirarin cewa, kasar Sin ita ce babban kalubale ga tsarin kasa da kasa na dogon lokaci, Yana mai cewa, a matsayinta na kasar da ta tsaya tsayin daka wajen kare tsarin kasa da kasa, kullum kasar Sin tana nacewa wajen ganin cewa, ya kamata dukkan kasashe su martaba tsarin kasa da kasa tare da MDD a matsayi jagora, da tsarin kasa da kasa bisa dokokin kasa da kasa, da kuma muhimman dokokin tafiyar da dangantakar kasa da kasa bisa manufofi da ka'idojin yarjejeniyar MDD

Daga nan Wang ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta yi imanin cewa, kamata ya yi huldar dake tsakanin kowace kasa ta kasance bisa daidaito, da tuntuba, da fahimtar juna, kana ya kamata dukkan kasashe, su daidaita makomar duniya tare. Tsarin hadin gwiwar kasashen dake yankin tekun Indiya da Pasifik da Amurka ta kaddamar wani salo ne na kafa wani gungu, wanda kuma ba zai taba yin nasara ba. (Ibrahim)