logo

HAUSA

Ya kamata kasashen BRICS su hada gwiwa kan ci gaban fasahohin zamani

2022-05-25 10:30:32 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin Wang Yong ya ce, ya kamata kasashen BRICS sun yi amfani da damar dake akwai daga ci gaban fasahohin intanet, wajen zurfafa hadin gwiwarsu a fannin.

Wang Wong ya bayyana haka ne a taron kungiyar BRICS kan raya fasahohin sadarwar intanet da kirkire-kirkiren na’urori, wanda aka fara jiya a birnin Xiamen na lardin Fujian dake kudu maso gabashin kasar Sin.

Ya kara da cewa, a shirye Sin take ta hada hannu da sauran kasashen BRICS wajen inganta raya fasahohin sadarwar intanet da kirkire-kirkiren na’urori, da samu ci gaba mai inganci da juriya kuma mai dorewa tare. (Fa’iza Mustapha)