logo

HAUSA

Sin: Amurka ta kirkiro karairayi don ta boye karyar da ta yi

2022-05-25 20:02:15 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau cewa, tun farko Amurka ta bukaci babbar kwamishiniyar hukumar kare hakkin dan-Adam ta MDD da ta ziyarci jihar Xinjiang, amma kuma yanzu tana adawa da ziyarar da babbar jami’ar hukumar ta kai kasar Sin.

Amsar rashin fahimtar juna da Amurka take yi abu ne mai sauki, wato Amurka tana tsoron kasashen duniya su fahimci karyar da ta yi game da kisan kiyashi da aikin tilastawa jama'a a jihar Xinjiang, don haka ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen kirkiro karairayi, don neman bata sunan kasar Sin domin ta yaudari kasashen duniya.

Wang Wenbin ya kara da cewa, Amurka ta keta manufar kasar Sin daya tilo a duniya, da tunzura, da goyon bayan ayyukan ‘yan aware masu neman ‘yancin Taiwan a asirce, wanda hakan ba zai haifar da da mai ido ba ga dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka. (Ibrahim)