logo

HAUSA

Wang Yi zai ziyarci kasashen tsibirin kudancin tekun Pasifik da Timor ta Gabas

2022-05-24 19:08:38 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya sanar da cewa, mamban majalisar gudanarwa kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, zai ziyarci tsibirin Solomon, da Kiribati, da Samoa, da Fiji, da Tonga, da Vanuatu, da Papua New Guinea da kuma Timor ta Gabas daga ranar 26 ga watan Mayu zuwa 4 ga watan Yuni.

Haka kuma Wang Yi zai kai ziyara zuwa Tarayyar Micronesia, inda zai gana ta kafar bidiyo tare da firaminista da ministan harkokin wajen Tsibirin Cook, da firaminista da ministan harkokin wajen Niue, kana zai jagoranci taron ministocin harkokin wajen kasashen Sin da tsibiran Pacific karo na biyu da zai gudana a Fiji.

Wang Wenbin ya kara da cewa, kasashen Amurka, da Birtaniya da sauran kasashe, na neman yin amfani da ziyarar da babbar jami'ar hukumar kare hakkin dan-Adam ta MDD ta ke yi a kasar Sin, wajen yada abin da ake kira "batun Xinjiang" da kuma neman bata sunan kasar Sin.

Ya kara da cewa, kasashen Japan da Amurka, sun dage kan jirkita batutuwan da suka shafi kasar Sin, da takala da neman bata sunan kasar Sin, da kuma tsoma baki a harkokin cikin gidanta. Kasar Sin ta bayyana rashin gamsuwarta da ma adawa da hakan. (Ibrahim)