logo

HAUSA

Labarin Xi Jinping Da Mahaifinsa

2022-05-24 10:27:25 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce “Ina fatan kara koyon kyawawan dabi’u masu daraja daga mahaifina”. Mahaifinsa Xi Zhongxun, “wani jagoran al’umma ne wanda ya samo asali daga al’umma”. Ya kan ce shi da ne na manomi, wanda har kullum ya kan maida shi kansa a matsayin daya daga cikin al’umma. Duk wanda ke kaunar al’umma da samar musu da alheri, al’umma za su maida shi tamkar dan uwansu. Samo asali daga al’umma, da kuma sake dawowa cikin al’umma, shi ne ainihin buri na farko na Xi Jinping da na mahaifinsa.

A lokutan juyin juya hali daban-daban, Xi Zhongxun ya kan lura da al’umma sosai, yana dora muhimmanci kan ainihin muradunsu.

Dogara kan al’umma, da bauta musu, nauyi ne da Xi Jinping da mahaifinsa suka dauka tare.

Tun da aka shirya babban taro karo na 18 na wakilan jam’iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin, kawo yanzu, shugaba Xi Jinping ya yi tattaki zuwa wurare 14 masu fama da matsanancin talauci a kasar, ya gudanar da nazari kan ayyukan yaki da talauci sama da sau 50, inda ya sauke nauyin tarihi dake wuyansa, tun daga ganewa idanunsa ainihin talaucin da ake fama da shi, har zuwa daukar matakai na zahiri don yaki da talaucin.

A ranar 25 ga watan Oktobar shekara ta 2017, a wajen cikakken zama na farko na kwamitin koli karo na 19 na jam’iyyar kwaminis, Xi Jinping ya bayyana cewa: “Jam’iyyar kwaminis gami da al’umma, sun mika wannan babban aiki gare mu, saboda amincewa da kyakkyawan fatansu gare mu. Bai kamata mu manta da burinmu tun farkon farawa ba, da sauke babban nauyinmu, mu yi aiki tukuru, don bautawa jam’iyya gami da kasarmu baki daya, da bayar da gudummawa wajen gina al’umma mai matsakaiciyar wadata daga dukkan fannoni, da samun nasarar raya kasa mai tsarin gurguzu irin na salon musamman a sabon zamanin da muke ciki.”  (Murtala Zhang)