logo

HAUSA

Wang Yi ya halarci bikin kaddamar da taron shekara-shekara na ESCAP karo na 78 ta kafar bidiyo

2022-05-23 19:02:01 CMG Hausa

Yau ne, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya halarci bikin kaddamar da taron shekara-shekara na hukumar tattalin arziki da zaman takewar al’umma ta yankin Asiya da tekun Pacifik ta MDD wato ESCAP karo na 78 ta kafar bidiyo a birnin Guangzhou, fadar mulkin lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin, inda ya gabatar da jawabi.

Cikin jawabinsa, Wang Yi ya bayyana cewa, ya dace a hada kai domin gina kyakkyawar makomar kasashen yankin Asiya da tekun Pacifik, ta hanyar daukar matakai uku, na farko, nacewa kan manufar kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali, tare kuma da nuna adawa ga yunkurin tayar da hankali a tsakanin rukunonin aikin soja cikin yankin na Asiya da tekun Pacifik, na biyu, sanya kokari tare domin ingiza ci gaban tattalin arziki, da gina yankin ciniki maras shinge a yankin, na uku, kasashen da abin ya shafa dake yankin, su hada kai domin gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsu, ta yadda za su cimma burin samun moriya tare.

Kana Wang Yi ya jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace, domin ba da karin gudummowa kan tabbatar da dauwamammen ci gaba da kwanciyar hankali mai dorewa a yankin. (Jamila)