logo

HAUSA

Sin ta himmatu wajen tabbatar da kafuwar yankin ciniki maras shinge na Asiya da Pacific

2022-05-23 10:31:17 CMG Hausa

Ministan ma’aikatar cinikiyya ta kasar Sin Wang Wentao, ya ce kasar sa za ta yi aiki tukuru, wajen tabbatar da nasarar kafa yankin ciniki maras shinge na Asiya da Pacific, cikakke kuma bisa matsayin koli.

Minista Wang ya bayyana hakan ne cikin jawabinsa ta kafar bidiyo, yayin taro na 28 na ministocin kungiyar hadin gwiwar raya tattalin arzikin yankin Asiya da Pacific ko APEC, wanda ya gudana a karshen mako.

Wang ya ce kamata ya yi dukkanin kasashe mambobin APEC su jajirce, wajen gina al’umma mai makomar bai daya a matsayin tushensu, su kuma ingiza hadin gwiwa na zahiri a sassa daban daban na cinikayya da zuba jari.

Ministan ya kara da cewa, kasar Sin za ta kara bude kofofinta tare da ci gaba da samar da matakan daidaita ci gaban tattalin arzikin duniya da na shiyyoyi.

Ya ce Sin na aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar hadin kai ta raya tattalin arzikin yankin da take bisa inganci, tana kuma aiwatar da matakin gina yankin ciniki maras shinge na Asiya da Pacific mai matsayin lamba 3.0, tare da sauran kasashe mambobin kungiyar ASEAN.

Bugu da kari, tana ci gaba da yayata amincewarta da cikakkiyar yarjejeniyar hadin gwiwar raya tattalin arzikin zamani ta kasashen yankin Pacific.

Daga nan sai minista Wang, ya jaddada cikakken goyon bayan kasar Sin, ga tsarin cinikayyar sassa da dama, karkashin lemar kungiyar cinikayya ta duniya WTO, da tabbatar da tsaro da daidaito a fannin sarrafawa da samar da hajoji, tare da gabatar da karin gajiya ga dukkanin sassa.  (SAMINU)