logo

HAUSA

An samu sabbin mutane 169 da suka kamu da COVID-19 a babban yankin Sin

2022-05-22 17:44:34 CMG Hausa

 

Bisa alkaluman da hukumar kula da lafiyar kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, an samu mutane 169 da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a babban yankin kasar a ranar Asabar.

Daga cikin adadin, 157 na da alaka da yada cutar a cikin gida, sannan 12 kuma daga ketare.

An samu jimillar sabbin kamuwa da cutar 729 wadanda basu nuna alamomin kamuwa da cutar ba a ranar Asabar, yayin da adadin majinyatan da basu nuna alamun kamuwa da cutar ba 37,636 suke karkashin kulawar jami’an kiwon lafiya.

Kawo yanzu, adadin mutanen da aka tabbatar sun taba kamuwa da cutar COVID-19 a babban yankin kasar Sin ya kai 223,145, sannan jimillar mutane 5,222 annobar COVID-19 ta kashe a kasar.(Ahmad)