logo

HAUSA

Gwamnatin Sin za ta baiwa manoman hatsi rangwamen yuan biliyan 10

2022-05-22 16:14:35 CMG Hausa

Kwanan baya, gwamnatin kasar Sin ta tsai da kuduri cewa, za ta baiwa manoman dake shuka hatsi kudin Sin Yuan biliyan 10 sakamakon karuwar farashin kasuwar kayayyakin da manoman ke bukata, da yanayin aikin gona da kasar ke ciki.

Rahotannin sun nuna cewa, an samar da kudin ne domin goyon bayan aikin girbin hatsi a yanayin zafi da aikin shuka hatsi a yanayin kaka, saboda farashin kayayyakin da manoma ke bukata yayin gudanar da aikin gona ya karu, ta yadda za a kara karfafawa manoma gwiwa.

A sa’i daya kuma, ma’aikatar kudin kasar Sin za ta kara kyautata manufar samar da rangwame, domin tabbatar da cewa, za a baiwa manoman dake shuka hatsi kudin yadda ya kamata. (Jamila)