logo

HAUSA

Sin za ta gaggauta raya tsarin lambunan shan iska da na tsirrai

2022-05-21 17:28:31 CMG Hausa

Rahotanni daga bikin tallata ranar kasancewar halittu daban-daban na duniya na shekara ta 2022 wanda aka yi a jiya Jumma’a a kasar Sin sun ce, kasar za ta gaggauta raya tsarin lambunan shan iska da lambunan tsirrai, kuma a shekarar da muke ciki, za ta kara gina wasu lambunan shan iska, da kammala tsara shirin raya lambunan tsirrai na kasa.

Babban taken ranar kasancewar halittu daban-daban na duniya a bana shi ne, raya halittu masu kyakkyawar makoma ta bai daya a duniya. Sakamakon kokarin da aka yi na tsawon shekaru, kasar Sin ta riga ta gina tsarin kiyaye muhalli, dake kunshe da lambunan shan iska da yankunan kiyaye muhallin halittu da sauransu, al’amarin da ya sa ta kiyaye nau’ikan muhallan halittu na kasa sama da kaso 90 bisa dari, da kaso 71 bisa dari na dabbobi da tsirrai masu darajar gaske a kasar. (Murtala Zhang)