logo

HAUSA

MOC: Dalilan da ke jawo jarin waje a kasar Sin ba su canja ba

2022-05-20 10:52:59 CMG Hausa

Bayanai na baya-bayan nan da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, daga watan Janairu zuwa Afrilun bana, karuwar jarin waje a kasar, ya kai kashi 20.5 cikin 100 dangane da babban tushen ci gaban da aka samu a bara. Babban jami’i a ma’aikatar ya bayyana a ranar 19 ga wata cewa, tushen ci gaban tattalin arzikin kasar yadda ya kamata na matsakaici da dogon lokaci bai canza ba. Kasuwannin cikin gida na da girma sosai, kuma kamfanonin kasashen waje suna da kyakkyawan fata, game da hasashen ci gaba na dogon lokaci a kasar Sin.

Da dama daga cikin dalilan dake jawo hankalin masu zuba jari daga ketare, ba su canza ba. Ma'aikatar kasuwanci za ta yi aiki tare da dukkan yankuna da sassan da abin ya shafa, don ci gaba da yin kokari da nufin daidaita harkar zuba jari na ketare, da samar da yanayi mai kyau da ingantacciyar hidima ga kamfanonin ketare dake kasar Sin. Kamfanoni da dama na ketare sun nuna cewa, duk da tsaikon da aka samu na gajeren lokaci, jarin da suke zubawa a kasar Sin, ba zai canja ba, kuma za su ci gaba da nuna kwarin gwiwa game da makomar ci gaban kasar Sin. (Yaya Ibrahim)