logo

HAUSA

Mai ba MDD shawara ta damu da kama masu zanga-zanga da ake zargi da aikata laifin kisa a Najeriya

2022-05-20 11:26:51 CMG Hausa

Mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric, ya bayyana a jiya Alhamis cewa, mai ba MDD shawara Alice Wairimu Nderitu, ta bayyana damuwarta kan zanga-zangar da aka yi a Najeriya, don nuna rashin amincewa da kama wasu da ake zargin da kashe wata mata da ake zargin da yin sabo.

Stephane Dujarric, babban mai magana da yawun babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana cewa, Alice Wairimu Nderitu, mai ba da shawara ta musamman kan kandagarkin kisan kare dangi, ta kadu matuka da kisan Deborah Samuel, bisa zarginta ta yin batanci ga addinin musulunci ranar 12 ga watan Mayu a jihar Sokoto dake tarayyar Najeriya.

Wairimu Nderitu ta mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan Deborah Samuel, sannan ta bukaci hukumomi, da su gurfanar da wadanda suka aikata wannan danyen aiki a gaban kuliya.

Dujarric ya ce, jami’ar ta kuma damu da zanga-zangar da aka ce an gudanar wadda kuma ta kai ga haddasa barna a Sokoto, don nuna rashin amincewa da kama wasu daga cikin wadanda suka aikata wannan danyen aiki. Don haka, tana fatan hakan ba zai hana jami'an tsaro gudanar da aikinsu kan wadanda ake zargi da aikata laifin ba. (Ibrahim)