logo

HAUSA

Iraki za ta inganta musaya ta abota da hadin gwiwa da kasar Sin

2022-05-18 10:30:16 CMG Hausa

Shugaban Iraki Barham Salih ya ce, kasarsa za ta kara inganta musaya ta abota da hadin gwiwa da kasar Sin a fannoni daban-daban domin amfanawa kasashen biyu.

Wata sanarwar da ofishin jakadancin Sin a Iraki dake da mazauni a birnin Baghdad ya fitar, ta ce shugaba Salih, ya bayyana haka ne yayin ganawarsa da Cui Wei, wanda ya gabatar da kansa a matsayin sabon jakadan Sin a kasar.

Har ila yau, shugaban na Iraki, ya yabawa dadaddiyar dangantakar dake tsakanin Iraki da Sin, yana mai alkawarin bunkasa kawancen kasashen biyu da kara kaimi wajen musayar al’adu da mu’amala tsakanin jama’arsu da zurfafa hadin gwiwa wajen gina Ziri Daya da Hanya Daya, ta yadda kasashen biyu da jama’arsu za su amfana.

A nasa bangaren, jakadan kasar Sin Cui Wei ya ce, cikin watan Augustan bara, shugabannin kasashen biyu sun cimma matsaya kan wasu muhimman batutuwa na zurfafa kawance da inganta hadin gwiwarsu domin samun karin ci gaba da share fagen hanyar bunkasa dangantakar dake tsakaninsu. (Fa’iza Mustapha)