logo

HAUSA

Wang Yi zai jagoranci taron ministocin wajen kasashe mambobin kungiyar BRICS ta kafar bidiyo

2022-05-18 20:32:10 CMG Hausa

A gobe Alhamis ne babban dan majalissar gudanarwa, kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, zai jagoranci taron ministocin wajen kasashe mambobin kungiyar BRICS ta kafar bidiyo.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ne ya sanar da hakan a yau labara, yana mai cewa, taron na gobe zai hallara ministar ma’aikatar hulda da kasashen waje da hadin gwiwa na Afirka ta kudu Naledi Pandor, da ministan wajen Brazil Carlos Franca, da na Rasha Sergey Lavrov, da na India Subrahmanyam Jaishankar.

Yayin taron, ministocin wajen kasashe mambobin na BRICS, za su tattauna karkashin inuwar dandalin "BRICS+", tare da abokan huldar kungiyar na kasashe masu karsashin tattalin arziki, da na kasashe masu tasowa. (Saminu)