logo

HAUSA

Babban mai ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin ya jaddada bunkasa tattalin arziki na zamani

2022-05-18 11:10:04 CMG Hausa

Babban mai ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin Wang Yang, ya yi kira da a ci gaba da kokarin bunkasa tattalin arziki na zamani.

Wang ya bayyana hakan ne a wani taron tuntuba da kwamitin CPPCC na kasa ya gudanar a nan birnin Beijing.

Masu ba da shawara da masana harkokin siyasa 29 ne suka yi jawabi a yayin taron, yayin da masu ba da shawara kan harkokin siyasa sama da 140 suka bayyana ra'ayoyinsu ta hanyar wayar hannu.

Daga nan, sai suka yi kira da a samar da manyan ci gaba a manyan fasahohin zamani, don kiyaye ’yancin cin gashin kansa na bunkasa tattalin arziki na zamani, bisa la’akari da fa'idar hukumomin kasar da kuma girman kasuwanninta. (Ibrahim)