logo

HAUSA

EFCC ta tsare Akantan Janar na Najeriya

2022-05-17 21:30:38 CMG Hausa

Hukuma mai yaki da zamba da masu yiwa tattalin arziki ta’annati a Najeriya, ta tsare Akanta Janar na kasar Ahmed Idris, bisa zargin sa da karkatar da kudaden gwamnati, da kuma safarar kudade.

A cewar kakakin hukumar ta EFCC Wilson Uwujaren, sun kama Idris ne a jiya Litinin, bayan da ya ki amsa gayyatar da hukumar ta yi masa, domin ya amsa wasu tambayoyi masu nasaba da zambar kudaden da yawan su ya kai naira biliyan 80, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 193.  (Saminu)