logo

HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen Sin: Sanarwar G7 kan batun kasar Sin karya ce zalla

2022-05-16 20:36:02 CMG Hausa

A kwanan nan ministocin harkokin wajen kasashen G7 sun fitar da wata sanarwa, wadda a cikin ta aka ambaci batun da ya shafi kasar Sin sau da dama.

A game da wannan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Zhao Lijian ya bayyana cewa, kasarsa ta bukaci kasashen G7 da su kiyaye tsarin kasa da kasa karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya, da mutunta ikon mulkin kai na kasar, tare kuma da dakatar da shafawa kasar bakin fenti, da yin shisshigi cikin harkokin cikin gidanta.

Zhao ya kara da cewa, kasarsa ta bukaci kasashen G7 su maida hankali kan wanzar da zaman lafiya, da samar da ci gaba a duniya, da daina amfani da “ma’aunai biyu”, ko kuma fiye da haka, da dakatar da yiwa sauran kasashe barazana ta hanyar tura jiragen saman yaki, da jiragen ruwan yaki, da daina hura wutar rikici a sauran kasashe, da kuma dakatar da sanyawa sauran wasu kasashe takunkumi ba gaira ba dalili, da daina yayata jita-jita game da kasar Sin. (Murtala Zhang)